Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa al’ummar jihar Bauchi bisa ibtila’in gobara a da lamushe babbar Kasuwar Azare a yankin Katagumna jihar Bauchi. Haka kuma Shugaban ya jajantawa Gwamnati da al’ummar jihar bisa iska mai karfi da ta yi barna a kwanakin baya.

Shugaban yace a madadinsa da Gwamnatin tarayyar Najeriya suna mika sakon jajensu ga wadan da wannan bala’n ya shafa. Ya kuma yi adduar Allah ya kareaukuwar hakan nanan gaba.

Ya kara da cewar “Duk wani mai imani dole hankalinsa ya tashi idan yaji labarin yadda iska mai karfi tare da ruwan sama suka yi barna a yankunan jihar Bauchi, ga kuma gobara da ta lashe kasuwar Azare” A cewar SHugaba Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY