Daga Hagu zuwa dama, Shugaban jam'iyyar APC na kasa John Odigie-Oyegun sai Shugaban kasa Muhammadu Buhari sai mataimakinsa Yemi Osibanjo sai Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki sai Sakataren jam'iyyar Mai-Mala Buni

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu akan batunkarin wa’adin shekara guda da aka yiwa Shugaban jam’iyyar APC na kasa John Oyegun,inda yace hakan ya sabawa tsarin mulkin jam’iyyar.

DAILY NIGERAIN ta tabbatar da cewar Mista Tinubu, wanda yake jagorantar kwamitin sulhunta ‘yan jam’iyyar APC masu samun sabani da juna, yana zaman doya da manja tsakaninsa da Shugaban jam’iyyar John Oyegun.

Da yake magana a wajen taron Shugabannin majalisar koli na jam’iyyar a ranar Talata, Shugaba Buhari ya ce karawa Shugabannin jam’iyyar wa’adin shekara guda ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar dama kundin tsarin mulkin Najeriya.

 

LEAVE A REPLY