Yusuf Buhari tare da Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa ga ‘yan Najeriya maza da mata yadda suka nuna tausayawa ga dan sa Yusuf Buhari a lokacin da ya samu hadari a kwanakin baya, a yanzu haka dai an sallami Yusuf daga Asibiti kuma ya koma gida.

Femi Adesina mai taimakawa Shugaban kasa akan kafafen yada labarai, ya bayyana wannan sako na Shugaba Buhari a ranar Juma’a.

Sakon yana cewa “Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai dakinsa Aisha Buhari da dukkan dangi da iyalansa suna nuna matukar godiya ga al’ummar najeriya bisa tausayawa da suka nuna a lokacin da Yusuf Buhari ya gamu da ibtila’i”

 

LEAVE A REPLY