Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gana da Gwamnonin jam’iyyar APC a shirye shiryen babban taron jam’iyyar na kasa karo na farko tun bayan da ta kama mulki a shekarar 2015.

Shugaba Buhari yayi tattaunawarda Gwamnonin ne cikin sirri ba tare da barin ‘yan jaridu sun halarci tattaunawar ba, wadda ta kasance a fadar Shugaban kasa dake Villa a babban birnin tarayya dake Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya habarto cewar, taron ana sa ran zai fi mayar da hankali ne akan batun babban taron jam’iyyar na kasa da zai gudana nan ba da jimawa ba, wanda aka tsara yi a ranar 14 ga watan Mayu mai zuwa a Abuja.

Tuni dai uwarjam’iyyar APC ta kasa ta rubutawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC cewar zata gudanar  da babban taronta, tare kuma da zabe sabbin Shugabanni a duk fadin Najeriya.

Idan ba’a manta ba, a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyarda ya gudana a sakatariyar jam’iyyar Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa zaben Shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar a 2019.

Wadan da suka halarci wannan tattaunawa sun hada da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo da kuma Sakataren gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha da kuma Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Abba Kyari.

Sauran kuma sun kunshi Gwamnonin APC da suka hada da Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Abdullahi Umar na jihar Kano da Yahaya Bello na jihar Kogi da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara da kuma Jibrila Bindow na jihar Adamawa.

Ragowar sune,  Simon Lalong na jihar Filatu da Rochas Okorocha na jihar Imo da Kashem Shettima na jihar Borno da Abubakar Sani Bello na jihar Neja da Tanko Almakura na jihar Nasarawa da Abiola Ajimobi na jihar Oyo da Ibikunle Amosun na Ogun da Godwin Obaseki na jihar Edo da kuma Abubakar Badaru na jihar Jigawa.

NAN

LEAVE A REPLY