Festus Keyamo SAN, wanda a kwanakin baya aka nada shi a matsayin Kakakin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Buhari da Osinbajo na zaben 2019. Shugaban kasa ya kuma gwangwaje shi tare da wasu mutum shida, da mukamin bod mamba na hukumar NDIC ta kasa.

Festus Keyamo an bashi wannan mukami ne domin ya wakilci jihar Delta a matsayin bod mamba.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya karanta da aka aiko daga fadar Shugaban kasa,inda ake neman sahalewar majalisar domin nadin nasu a sabon mukamin.

LEAVE A REPLY