Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai shiga tsakanin Kwankwaso da Ganduje domin sasanta su.

A kokarinsa na dinke barakar da ake fama da ita a jam’iyyar APC, Shugaba Buhari ya nada tsohon Gwamnan jihar Legas wanda kuma ake ganin shi ne jagoran APC a Najeriya baki daya, Bola AHmed Tinubu.

Mai taimakawa Shugaban kasaa kaan hulda ba kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayar da wannan sanarwa a ranar talata.

A cewar Garba Shehu, wannan aikin da aka baiwa Tinubu ya shafi magance dukkan wata damuwa da take tsakanin manyan ‘yan Siyasar biyu, dama sauran jihohin da ake fama da rikicin cikin gida a jam’iyyar ta APC.

Rikicin da jam’iyyar APC ta ke fama da shi a jihar Kano ya jefa magoya bayan tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje cikin wani mawuyacin hali, a sabida haka ne Tinubu zai jagoranci sasantawa.

A ranar 29 ga watan Janairu fadar Shugaban kasa ta gayyaci Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kan batun hana Kwankwaso zuwa Kano da aka yi a ranar 30 ga watan da ya gabata domin gudun barkewar rikici a cewarsu.

Gwamnan wanda yaje fadarShugaban kasa tare da rakiyar Sanatocin Kano guda biyu da kuma ‘yan majalisar tarayya, sun gana da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Malam Abba Kyari.

Gwamna Ganduje yaki cewa komai ga ‘yan jarida yayin da ya fito daga waccan ganawa a fadar Shugaban kasa dake Aso Rock Villa.

Ana sa ran wannan kwamiti da Tinubu zai jagoranta zai sasanta rikita rikitar jam’iyyar APC a jihohin Zamfara da Oya da kuma Kogi.

NAN

LEAVE A REPLY