Shugaban kasa Muhammadu Buhari

A yayin zaman majalisar zartarwa na Gwamnatin tarayya ranar Laraba a fadar Shugaban kasa, Shugaba Buhari ya amince a kashe naira biliyan 72.9 domin gina titi mai layi goma a jihar Legas titin da ya tashi daga unguwar Apapa ya hade da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Ministan dake kula da ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da lantarki Babatunde Fashola ne ya sanar da hakan ga ‘yan jaridun dake fadar Shugaban kasa yau bayan kammala zaman majalisar na wannan makon.

Fashola yace, wannan dai wani muhimmin aiki ne da aka jima ana fatan samunsa, domin saukaka harkar sufuri da kuma rage cunkoso a jihar ta Legas.

LEAVE A REPLY