A shirye shiryen bikin cikar Gwamnan jihar Zamfara Mai daraja Abdulaziz Yari Abubakar shekaru 7 akan kujerar Gwamnan jihar, ana sa ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbaji zasu kaddamar da ayyukan da suka hada da hanyoyi da makarantu da asibitoci da sauransu.

Alhaji Lawal Liman, shugaban kwamatin gudanar da wannan biki shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba a Gusau babban birnin jihar.

Ya kara da cewar, dukda ba’a sanya ranar da Shugaban kasa zai zo jihar ba, amma dai zai zo din domin kaddamar da ayyukan raya kasa da gwamnatin Abdulaziz Yari ta yi a jihar a tsawon wa’adin mulkin da yayi na shekaru bakwai.

Haka kuma,ana sa ran Ministoci da manyan mukarraban Gwamnati suma zasu zo jihar ta Zamfara domin kaddamar da manyan ayyukan da Gwamnan jihar yayi a cewar sanarwa.

LEAVE A REPLY