Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar talata ya bayyana dalilan da suka sanya shi kin halartar taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka yi wanda ya samu halartar Shugaba Muhammadu Buhari dda Gwamnoni da Shugaban majalisar dattawa da kuma ‘yan majalisun dokoki na kasa a babban dakin taro dake fadar Shugaban kasa a Abuja.

Acewar jagoran jam’iyyar na kasa, kin halartarsa taron a fadarShugaban kasa ba wani abu bane da ya kamata ace ya ja hankali har ana tattauna shi.

Yace, wasu matasa ne a cikin shirye shiryen bikin zagayowar ranar haihuwarsa suka shirya wani kwarya-kwaryar taro a birnin Legas a ranar Litinin kuma suka bukaci lallai sai ya halarta.

Mai magana da yawun jagoran APC na kasa Bola Ahmed Tinubu,Mista Tunde rahman shi ne ya bayyana hakan aLegas.

LEAVE A REPLY