A kalla mutane takwas ne ake sa ran sun mutu a sanadiyar wata gwabzawa da aka yi tsakanin rundunar sojojin Najeriya da kuma mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Yobe dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Wata majiyar rundunar soojin ta tabbatar da cewar a lokacin da jami’an sojojin suke aikin sintiri a jihar Yobe din ne ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka yi musu kwanton bauna, inda daga nan suka fara musayar harbe harbe.

Wani jami’in rundunar sojin ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewar sojojin da ‘yan Boko Haram din suka kashe suna iya fin takwas ma in za’a yi kididdiga, baya ga kuma sojojin da suka ji munanan raunuka wadan da suke bukatar kulawar gaggawa.

Haka kuma, kakakin rundunar Lafiya Dole, Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya bayyana cewar an samu wadan da suka ji munanan raunuka, sai dai yaki ya bayyana cewar ko soja sun mutu ko basu mtu ba.

 

LEAVE A REPLY