Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam

Hassan Y.A. Malik

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Abdulmaliki Sumonu, a jiya Litinin ya tabbatarwa manema labarai cewa, wasu da ake zargi ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kan garin Dapchi, helikwatar karamar hukumar Busari ta jihar Yobe.

Sumonu ya tabbatar da hakan ne a wata hira da ya gabatar da kamfanin dillacin labarai (NAN).

Ya ce, “Da misalin karfe 5:30 na yammacin yau (jiya Litinin), maharan suka kai hari kan garin Dapchi, helikwatar karamar hukumar Busari.”

“Zuwa yanzu dai, bamu gama tattara hasarar da harin ya haifar ba tukunna,” kwamishina Sumonu ya ce.

Kwamishina ya ci gaba da cewa, tuni dai jami’an tsaro suka ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro a yankin da abin ya faru.

Rahoton da ya ke ishemu ya tabbatar mana da cewa, tuni ‘yan garin Dapchi suka tsere suka bar garin don tsira da rai da lafiya.

Shugaban karamar hukumar Busari, Alhaji Zanna Abatcha, ya fadawa manema labarai cewa, maharan tuni sun bar garin kuma jami’an tsaro a halin da ake ciki sune ke rike da ragamar tsaron garin, wanda hakan ya sanya tsaro ya dawo a yankin.

Sai dai har yanzu ba a gama tantance iya ta’adain da maharan suka yi a garin na Dapchi ba, kuma da zarar bincike ya kammala, za a sanar da manema labarai.

LEAVE A REPLY