Akalla mutane 10 ne ake jin cewar sun halaka, yayinda mutane 65 suka samu munanan raunuka a wani harin kunar bakin wake da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a birnin Maiduguri na jihar Borno.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, Abdukadir Ibrahim ya bayar, yace wata mace da ake kyautata zaton ta layyace jikinta da bom ce ta kai wannan harin.

“Tuni masu bayar da agajin gaggawa suka isa wannan wajen da aka kai harin, an kai wannan harin ne a tashar motar dake Muna dake kan hanyar Mafa Dikwa a birnin Maiduguri”

“Masu bayar da agajin sun kaiwa mutane 65 din da suka ji raunuka dauki,inda aka basu kulawa nan take, yayin da aka garzaya da su asibiti domin karbar magani. A kalla mutum 10 sun mutu a yayin wannan harin”

“Wani rahoto ya nuna cewar,ana jin cewar wasu mata su hudu da suka layyace jikinsu da bama bamai ne suka kai wannan harin”

“Lamarin ya auku da misalin karfe 5:05 na yammacin ranar laraba”

 

LEAVE A REPLY