Daga Hassan Y.A. Malik

Mazauna yankin Soluyo/Sosanya da ke Gbagada a jahar Lagos sun fara tserewa daga gidajen su a sakamakon mamaye yankin da birrai suka yi.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun fadawa kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a yau Litinin cewa wannan lamarin birran na matukar ci masu tuwa a kwarya.

Shugaban kungiyar mazauna yankin, Mista Adigun Olayeye ya fadawa manema labarai yadda birran ke shiga masu gidaje su ci masu abinci su lalata masu tagogi da ragar da suka sanya a kofofin su.

Ya ce birran na shigowa yankin ne daga jejin da ya raba su da yankin Ifako.

Olayeye ya ci gaba da cewa lamarin ya yi kamari har wasu mazauna yankin sun tattara ina su inasu sun sauya matsugunni.

Ya ce tuni suka rubuta takardar korafi zuwa ga ma’aikatar harkokin noma ta jahar amma har yanzu an yi biris da su.

A don haka ne ya yi kira ga gwamnatin jahar da ta yi wa Allah ta dubi halin da suke ciki ta kai masu dauki cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY