Daga Hassan Y.A. Malik

Wata runduna ta sojan Nijeriya da aka tura aikin tsaro a garin Idon Raini da ke kan hanyar Maganda zuwa Sofo zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna, ta yi nasarar ceto wasu mutum takwas da aka yi garkuwa da su aka boye a wata maboya ta masu garkuwa da mutane da suka addabi masu amfani da wannan hanya.

Ciikn wadanda sojojin suka ceto akwai maza 3, mata 2 da kuma yara kanana 3.

A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin kasa na Nijeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya fitar a jiya Talata, ya bayyana cewa rundunar ta su ta samu kwato wasu kayayyaki daga hannun wadannan bata gari da ke aikata sace mutane suna garkuwa da su akan hanyar Birnin Gwari da suka hada da mota kirar Golf mai launin ja, da mota kirar tirela da wasu akwatuna biyu dankare da suturu da ake zargin na wasu fasinjoji ne da masu garkuwa suka kama akan hanya.

Sanarwa ta bayyana cewa, sojojin sun sake kama wani mashin da wani mai garkuwa da mutane ya yar ya kuma tsere a lokacin da ya hangi tawagar sojojin sun nufa inda ya ke a lokacin da suke aikin faturu a kauyen Nachibi.

Haka kuma, a wata fitar aiki da sojojin suka yi zuwa kauyen Maidaro, an yi arangama tsakanin sojoji da bata gari a lokacin suna tsaka da gasa wata saniya. A fafatawar, ‘yan sintiri guda 3 sun samu  raunika daga harbin bindiga, inda aka yi nasarar kashe bata gari guda 1.

Birgediya Texas Chukwu ya yi kira ga al’umma da ta gaggauta sanar da jami’an tsaro a duk lokacin da suka yi arba da wani motsi da basu gamsu da shi ba

LEAVE A REPLY