Daga Hassan Y.A. Malik

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da ‘Yan Kwashi ta jihar Jigawa, honarabul Muhammad Gudaji Kazaure, ya yi jan hankali ga  maza a zaman majalisar ta jiya Alhamis, inda ya bayyana cewa in har aka bawa mata da yawa to fa lalle za su hanbare maza daga madafun ikon kasar nan.

Honarabul Gudaji ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke bada tasa gudunmawar a yayin da ake tattauna batun bayar da dama ga mata a matsayin a raya ranar mata ta duniya da aka yi bikinsa jiya a fadin duniya.
Gudaji ya bayyana cewa, a bayyane ya ke mata su ke juya mazaje a gidajensu, saboda haka basu dama su yi kan-kan-kan da maza za ta iya zama barazana ga maza.

Kodayake dai Gudaji ya ce yana goyon bayan gwamnati da ma maza da su bawa mata dama a harkokin siyasa, kasuwanci da ma sauran harkokin rayuwa saboda matukar tasirinsu wajen saisaita rayuwar maza, to, amma tsoro Gudaji daya shine na kar in har mata idonsu ya bude sakamakon damar da aka basu, su kawace madafun ikon kasar, kuma daga baya su zo su balbalta al’amura.

“Tosrona shi ne, mata dai su ne ke juya al’amuran maza a cikin gida, kaga in har aka basu dama da yawa ta yadda za su iya juya al’amura a cikin gida da kuma a waje, to watarana sune za su mamaye al’amura a kasar nan.”

“In har muka basu dama da yawa, wata rana za mu shigo wannan zauren majalisa mu samu mata sun mamaye ko’ina, wanda ko shakka babu daga karshe za su balbalta al’amura.”

Ga bidiyon:

https://youtu.be/hB4e4Mk4sOk

LEAVE A REPLY