Sabon zababben Shugaban kasar Laberiya, George Weah

A ranar litinin aka rantsar da sabon zababben SHugaban kasar Laberiya George Weah a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a babban birnin kasar Monrobiya, inda dubun dubatar mutane suka halarta ciki da wajen kasar.

Sai dai, kwana daya bayan rantsar da shi, ya fara yin nade naden mukaman Gwamnati. Inda ya nada wani tsohon Sanata Pro-Tempore Gbezohngar Findley a matsayin ministan harkokin wajen kasar.

Saurana mutanan da aka nada su ne Maj.-Gen. Daniel Ziankahn a matsayin Ministan tsaro, sannan sai Brig. Gen. Prince Johnson a masayin sabon Shugaban hukumar tsaron kasar, sannan sai Mr Nathaniel McGill  a matsayin minista mai lura da harkokin fadar Shugaban kasa.

Haka kuma, sauran su ne, Samuel Tweh a matsayin sabon ministan kudin kasar, saiminstan Shariar kasar Mr Charles Gibson. Wadannan sune sabbin nade naden da Shugaba Weah yayi ya zuwa yanzu, sannan ya bukaci Shugabanni ma’aikatun Gwamnati da su ciga ada rike mukamansu kafin wani lokaci nan gaba.

NAN

LEAVE A REPLY