A jihar Bauchi Matan da suka amfana da shirin nan na ciyar da ‘yan makaranta na Gwamnatin Tarayya abinci, sun bawa marad’a kunya a zaben cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu da ya gudana a yau.
Kusan dukkan rumfunan zaben da  ya gudana rahotanni sun nuna mata sun nunka maza fitowa kuma mafi akasarinsu ke nuna cewar zasu nuna sakayya kan tallafin da suka samu.
An hango shugabannin kungiyar YABA KYAUTA TUKWICI ta wadan da suka amfana da shirin ciyarwa da Npower da saurarnsu suna takiran mata da su fito domin kada kuri’a a zaben Sanatan Bauchi ta Kudu.
Mai tallafawa Gwamnan Bauchi a bangaren kungiyoyin da ba na Gwamnati ba da kuma bayar da tallafi na musamman Mansur Manu Soro ya bayyana cewar kimanin mutane 704,000 suka ci gajiyar shirin tallafin Gwamnatin tarayya a Jahar Bauchi.

LEAVE A REPLY