Sanata Dino Melaye

Sanatan APC mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattawan najeriya, Dino Melaye, ya bayyana cewar Gwamnatin Shugaba Buharu ta APC ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 11 a cikin shekara uku, yayin da ta zarta abinda Gwamnatin PDP ta karbo na Naira Tiriliyan 6 a cikin shekara 16.

A lokacin da yake magana a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewar Gwamnatin Buhari ta karbo bashin dala biliyan 5.5, inda yake kalubalantar tayaya wannan zunzurutun kudade zasu amfani matasan Najeriya.

Sanata Melaye yace “Gwamnatin tarayya ta ci bashin Naira biliyan 500 domin inganta rayuwar al’umma,amma bamu gomai kan hakan ba wajen ingantar rayuwar al’ummar”

“Ba tare da jin wani tsoro  ko shakkar wani ba, Jam’iyyar PDP a cikin shekaru 16 ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 6, yayin da Gwamnatin jam’iyyarmu ta APC ta ciwo bashi Naira Tiriliyan 11 a cikin shekaru uku kacal, ba tare da kuma wani shiri da zai taimaki rayuwar matasa ba”

“Da ace Shsugaban kasa ya amince da samar da hukumar Peace Corps da dubban matasa zasu samu aikin yi domin dogaro da kansu”

 

LEAVE A REPLY