Daga Najib Sani

Mahajjaciya daga jihar Bauchi ita ɗaya tilo aka bari a Ƙasa mai Tsarki saboda ta yar da fasfonta.

Sakataren zartarwa na hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Harɗawa, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin ɗin nan cewa mahajjaciyar ‘yar asalin ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa ce.

Sai dai sakataren zartawar bai fada wa manema labaran sunan matar ba.

Da yake bayani kan mafitar wannan mahajjaciya, Alhaji Harɗawa ya ce ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar ta Sa’udiyya na ƙoƙarin sake yi mata sabon fasfo.

Ya ce da zarar an mata sabon fasfon za ta dawo gida.

LEAVE A REPLY