Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai

Babban bankin dake sanya ido kan harkokin ciniki da msana’antu dake shiga da fitar da kayayyaki daga Najeriya zuwa kasashen waje, ya sha alwashin tallafawa jihar Kaduna cimma muradun kasuwanci da ta sanya a gaba.

Bankin ya sha alwashin taimakawa jihar ta fannin fitarda kayayyakin masana’antu zuwa kasashen waje da ake bukatar su.

Wannan labarin ya zo ne a wata sanarwa da daraktan kula da hulda da kasashen duniya na Bankin Obi Emekekwue yafitar a ranar Litinin.

An jiyo daraktan yana ruwaito Shugaban Bankin Benedict Oramahe yana bayyana hakan ne a birnin Alkahira na kasar Masar.

 

LEAVE A REPLY