Hukumar tsaro ta farin kaya SSS ta bankado wani shiri na ‘yan Shian na yunkurin yin garkuwa da jami’an tsaro a kokarinsu na maida martani kan cigaba da tsare jagoransu Zakzaky da ake yi a hannun jami’an tsaro.

Wata sanarwa da hukumar tsaron ta SSS ce ta bayyana hakan wadda jaridar DAILY NIGERIAN ta samu inda tace “Abn bankado wani shiri na ‘yan Shia na yin garkuwa da jami’an tsaro tare da iyalansu domin cigaba da nuna fushinsu da suke yi ga hukuma kan tsare jagoransu Zakzaky da aka yi”

“A saboda haka hukuma take kira ga jama’a da su kai korafin duk wani mjtum da suka gani a makwabtansu ko a kasuwanninsu wanda ba su yarda da shi ba” A cewar sanarwar.

LEAVE A REPLY