Daga Hassan Y.A. Malik

Akalla mutane 8 ne suka rasa rayukan su yayin da wata bakuwar cuta ta barke a kauyen Dungurawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa cutar ta barke ne a makon da ya gabata kuma tuni har ta ruda mutanen garin.

Wani mazaunin garin mai suna Malam Sulaiman Tafida ya fadawa manema labarai a jiya Talata cewa cutar ta kashe masa ‘ya’ya uku.

A fadar shi “‘Ya’yana biyu Umar da Khadija sun rasu a ranakun Juma’a da Asabar, shi kuma Ibrahim a yau ya rasu. Duk irin cuta daya suka yi na dan gajeran lokaci kafin su rasu”.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta yi gaggawar aika tawaga zuwa kauyen domin su tabbatar da gaskiyar rahotannin.

Kwamishinan lafiya na jihar, Kabiru Getso shi ya sanar da haka ta baki jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya, Isma’il Gwammaja a jiya Talata.

Ya ce da zarar sun kammala bincike game da lamarin, za su sanar da jama’a sakamakon.

LEAVE A REPLY