A ranar talata Sarki Salman na Saudiyya ya sanya hannu akan wani daftarin da ya baiwa mata iznin tuka mota a kasar.

A cewar wannan daftari, wannan daya ne daga cikin sauye sauye da suka shafi tattalin arziki da masarautar take aiwatarwa. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya ruwaito.

Idan ba a manta ba, an sha taqaddama a kasar ta saudiyya kan dokar da ta haramtawa mata tuka mota.

Shin ko ya dace a baiwa mata iznin tuka mota a kasa mai tsarki?

LEAVE A REPLY