An baiwa hammata iska tsakanin sojoji da ‘yan sanda akan titin Ada George dake birnin Fatakwal da sanyin safiyar Alhamis din nan, yayin da sojojin suka kama DPO na yankin Rumukpaakani, bayan da suka zarge shi da hannu wajen kisan abokin aikinsu.

Sojan da akakashe, wanda yake cikin kaki an harbe shi ne dab da caji ofis din ‘yan sanda dake Rumukpakani, ana kuma zargin wani dan sanda ne dake bakin aiki ya bude masa wuta.

Wannan lamari ya harzuka wasu sojoji da yawa inda suka fita a kungiyance suka yiwa caji ofis na ‘yan sandan tsinke, suka kama DPO din da kuma dan sandan da ake zargi shi ne ya budewa sojan wuta ya mutu har lahira.

LEAVE A REPLY