Martanin da jam’iyyar PDP a jahar Sokoto ta mayar dangane da irin yadda wasu da ake zargin magoya bayan APC ne suke yada jita-jita rashin jituwa a shafin zumunta na Facebook.

“Babu sabani ko rashin fahimta kowane iri a tsakanin tsohon gwamna jahar Sokoto Attahiru Bafarawa da Gwamna Tambuwal ko da wasu magoya baya na jam’iyyar PDP dangane yadda za a gudanar da tafiyar jam’iyyar PDP a jahar Sokoto.

Dukkan masu ruwa da tsaki, a madadin magoya bayansu sun zauna tare da amincewa da tsarin da akayi bisa mutunci da girmama juna don ciyar da jahar Sokoto gaba da ceto al’umma da kasa baki daya.

Tun kamin yau, PDP a jahar Sokoto tana mutanta Gwamna Tambuwal kamar yadda yake mutanta da girmama shugabanin jam’iyyar da dattawan ta a koyaushe suka hadu.

Wadanda suke yada karya da furofaganda na yin soki burutsu ne kawai, don neman abinci da tayar da fitina ga jahar Sokoto; akan haka ne aka dauke su a yanar gizo don neman cimma burin masu biyansu ga tayar da fitina da haddasa rashin jituwa.

Yayyan jam’iyyar PDP a jahar Sokoto masu biyayya da mutunci ne, sun dauki junansu a matsayin uwa daya uba daya da na Gwamna Tambuwal, suna yi masa biyayya da bashi goyon baya akan matakin ciyar da jahar Sokoto da wanzar da zaman lafiya maimakon kiyayya da hassada”

Sanarwa daga
Alhaji Kabir Aliyu
Sakataren Jam’iyyar PDP
jahar Sokoto

LEAVE A REPLY