Tsohon Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Attahiru Jega

 

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega, a yau Juma’a,ya bayyana cewa, dalili daya da ya hana karan dimokuradiyyar Nijeriya ya kai tsaiko shi ne sojanci da ya gurbata hakakinin dimokuradiyyar da muke aiki da ita, sakamakon kasancewar jiga-jigan ‘yan siyasar kasar rikidaddun ‘yan siyasa ne da a baya suka aiwatar da mulkin fir’aunanci a lokacin da suka mulki kasar a kakin soja.

“Mafi yawancin ‘yan siyasar Nijeriya za ka iya kiransu da ‘ungulu da kan zabo’, dalili kuwa shi ne, saboda sun koyi siyasa ne a karkashin mulkin soja, musamman ma a lokacin da Ibrahim Badamasi Babangida ya yi tsarin mulkin nan nasa na soja a matakin tarayya, sannan ‘yan siyasa a jihohi.”

“Yanzu ga shi sun dauki dabi’ar nan ta soja sun saka ta a harkar siyasa, inda siyasarmu ta zama ta ‘ko a mutu ko a yi rai’.”‘ inji Jega.

Jega ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa a wajen wani taron gabatar da lakca da cibiyar dimokuradiyya da ci gaba (Centre for Democracy and Development (CCD) a Abuja, inda aka tattauna akan Shekaru 30 na wanzuwar mulkin dimokuradiyya a Afirka.

Jega ya ci gaba da cewa, akwai kokonto matuka kan shin al’umma na cin ribar dimokuradiyya a Afirka ko a’a?

Jega ya bada fatawar cewa, a maimakon al’ummar Afirka ta amfana da romon dimokuradiyya, sai ya kasance dimokuradiyya na haifar da tashe-tashen hankula da rashin tabbas.

Wannan kuwa dalili bisa ga kasancewar mafi yawan dimokuradiyyar kasashenmu na Afirka, mulkin sojan ne ya tsuguna ya haifesu.

Abin takaici ne matuka ganin yadda rashin zaman lafiya, rashin tabbas, da zaman dar-dar da dasa shugabanni ta hanyar karfa-karfa ya baibaye dimokuradiyyarmu.

 Farfesa Jega, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su sake yi wa dimokuradiyya kallo na tsanaki, la’alla sa yi karatun ta natsu ta yadda za su aiwatar da ka’idoji da dokokinta a aikace, wanda shi ne kadai zai tabbatarwa da al’ummar kasar cin moriyar mulkin siyasa.

LEAVE A REPLY