Aisha Bello

Babbar akanta janar ta jihar Kano, Aisha Bello, a ranar Alhamis ta mika takardar yin murabus dinta daga kan mukaminta da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada ta. rahotannin sun nuna hakan na da alaka da kutse da katsalanda da wasu manya a Gwamnati suke yi mata a cikin ayyukanta.

Majiya mai tushe ta ce, Akantar ta taba mikawa Gwamna Ganduje takardar yin murabus dinta a shekarar da ta gabata, sabida yadda wasu jiga jigan Gwamnati ke mata katsalandan da hana ta yin ayyukanta, amma Gwamna Ganduje ya ki yadda da murabus dinta a lokacin.

Ita dai Aisha Bello ta taba zama Kwamishiniyar kasafin kudi da tsare tsare kafin daga bisani, a nada ta Babbar Akanta janar ta jihar Kano. Hukumar karbar koke koken korafin jama’a da yakin da cin hanci da rashawa ta jihar kano ta binciki akantar a bisa yadda ta fitar da kudi ba tare da iznin Gwamnan Kano.

Wata majiya ta tabbatarwa da DAILY NIGERIAN cewar, hukumar karbar korafi ta jihar Kano ta yiwa akantar binciken kwakwaf kuma bata sameta da kowane irin laifi ba.

“Akanta janar din da alamun ta fusata ne, sabida wadan da aka samu da laifi a binciken da aka yi mata sun wuce salun alun ba tare da an hukunta su ba” A cewar majiyar..

Takardar Murabus din Aisha Bello

A cikin takardar murabus din wadda DAILY NIGERIAN ta samu, Akantar bata bayyana dalilan da suka sanya ta yi murabus din ba.

LEAVE A REPLY