Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa kan abinda ya faru ranar Laraba a zauren majalisar dattawa, inda wasu ‘yan daba karkashin jagorancin sanatan da aka dakatarsuka kutsa kai cikin majalisar suka sace sandar majalisar.

Atiku ABubakar dai ya bayyana takaicinsa ne a shafinsa na facebook, inda ya nuna faruwar irin wannan al’amari babban hadari ne ga demokaradiyyar kasarnan, kuma abin kaico ne da Allah wadai abin da ya faru din.

“Na ji matukar kaduwa da abinda ya faru a zauren majalisar dattawa, wannan ba kawai cin fuska bane ga ‘yan majalisar, yana nuna mugun hadarin da demokaradiyyar kasarnan ta ke fuskanta matukar ba a dauki mataki ba”

“Idan ‘yan daba zasu iya tsallake dukkan shingen jami’an tsaro dake harabar majalisar su kutsa kai cikin zauren majalisar kuma su dauke sandar majalisar su gudu da shi, to wannan yana nuna cewar hadarin da ake ciki a kasarnan babba ne kwarai da gaske”

“Wannan abinda ya faru a majalisa babu wanda zai ji dadinsa sai mugun mutum da baya yiwa demokaradiyyar kasarnan fatan alheri, dan haka ne, muke Allah wadai da wannan abinda ya auku a zauren majalisar kasa”

Daga karshe Atiku Abubakar ya ja hankalin ‘yan siyasa da su zauna da juna lafiya su kuma sani abinda duk zaman lafiya bai bayar ba, tashin hankali ba zai bayarda shiba.

LEAVE A REPLY