rundunar ‘yan sanda ta kasa ta karyata rahotannin da jaridun Najeriya suka bayar na yin wata zanga zangar ‘yan sanda a birnin Maiduguri na jihar  Borno a ranar Litinin.

An ruwaito cewar ‘yan sandan sun yi wata zanga zangar ba safai ba ranar litinin, inda suke kiran a biyasu hakkokinsu na kusan wata shida da aka kasa biyansu, alhali ga matsin rayuwa suna fuskanta.

Akwai dai ‘yan sanda fiye da dubu goma dake jibge a jihar Borno sakamakon rikicin Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa. ‘yan sandan da suka zargi hukumar da kin biyansu hakkokinsu, bayan sun yi ta yin korafin a biyasu amma aka ki saurarensu.

Sai dai kuma, rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayyana cewar abinda ‘yan sanda suka yi a Maiduguri yau, ba zanga zanga bace, illa sun taru ne domin mika kokensu ga rundunar ‘yan sanda ta kasa.

LEAVE A REPLY