Gwamnan jihar Osun Alhaji Rauf Aregbesola

Gwamnan jihar Osun Alhaji Rauf Aregbesola ya ci alwashin cewar ba za’a bishi bashin komai ba a karshen wa’adin mulkinsa na biyu da zai kare a 26 ga watan Nuwamban wannan shekarar ta 2018.

Mista Argebsola ya bayyana hakan ne a sakonsa na sabuwar Shekara ga al’ummar jihar Osun da aka yada a kafafen yada labaran jihar a safiyar litinin.

“Wannan ita ce shekarar zabe a jihar Osun, wanda hakan ke nuna kawo karshen wa’adin mulki na biyu na Gwamnatina, kuma, za’a samu sabon Gwamnan da zai gaje ni. Wannan alkawari ne da na dauka cewar ba za’a bini bashin komai ba a karshen wa’adin mulkina”.

Gwamnan ya kuma bayyana cewar, yana tuntubar Shugabannida jagororin jam’iyyarsa ta APC, akan yadda zai samu mutumin kirki mai amana da zai gajeshi.

Gwamnan ya cigaba da cewar “A cigaba da neman shawarwarin da yake yi na Shugabanni da jagororin jam’iyyar APC, zamu tabbatar mun zabi mutumin da ba zai cuci jihar mu ba, zamu zabi mutum mai mutunci da sanin yakamata”

“wanda yake da ra’ayi da akida irin tamu, wanda kuma zai ciyarda jiharmu da al’ummarmu gaba ba tare da gajiyawa ko canza tsarin da muke a kansa”

Haka kuma, Gwamnan ya godewa al’ummar jihar bisa goyon baya da suke bashi, da kuma sadaukarwa da suke yi domin cigaban jihar a iya tsawon Shekaru bakwai da yayi a t matsayin Gwamnan jihar Osun.

Mista Aregbesola ya kuma yabawa ma’aikatan Gwamnatin jihar, yace domin da gudunmawarsu ne ayyukan Gwamnati a jihar suke tafiya yadda ya kamata.

Da yayi magana kan batun kasafin kudin shekarar 2018, Gwamnan ya sha alwashin aiwatar da kasafin 2018 dari bisa dari.

Sannan kuma, Gwamnan, ya bukaci al’ummar jihar da su dinga biyan haraji, domin da shi ne ake yin galibin ayyukan a jihar.

“Duk kan abubuwan da muke bukata kamar hanyoyin masu kyau, ingantaccen ilimi, sha’anin tsaro da kuma kyakkyawan yanayi domin ingantuwar rayuwar al’umma ta yau da kullum, duk wadannan sun ta’allaka ga Gwamnati ne, kuma galibi da goyon bayan al’umma da kuma dan abinda ake samu na haraji da kason Abuja ake aiwatar da su”

“Babu wani mahaluki da zai iya cika dukkan muradun al’umma har yayi dadidai da abinda suke so dari bisa dari”

“Wannan shi ne dalilin da ya sanya dole Gwamnatinmu ta yi dukkan kokari wajen cimma abubuwan da ta sanya a gaba domin ganin an biya alkawuran al’umma” A cewar Gwamna Aregbesola.

NAN

LEAVE A REPLY