Sanata Shehu Sani

Sanata mai wakiltar jihar kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani, ya bayyana cewar babu wani abu mai kama da zaben ‘kwangires’ da ya gudana a jihar Kaduna, a ranarAsabar din da ta gabata.

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook. Inda ya bayyana cewar duk wani wanda ya zo da jadawalin sunayen mutanan da aka zaba da sunan kwangires to karya kawai ya sharara a cewar sanata Shehu Sani.

“Wakilanmu a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, babu wanda ya bamu labarin gudanar  da zaben sabbin Shugabannin mazabu na APC a dukkan fadin jihar Kaduna, idan wani ya shiga daki ya zo da lis din sunaye to ba halastattu bane”

“Mune muke ikirarin canji, ta dole mu kawowa al’umma canji mai ma’ana, in ba haka ba kuwa zamu gani a kwaryarmu”

LEAVE A REPLY