Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da abinda ya faru na mamaye harabar shiga majalisar tarayya da jami’an tsaron DSS suka yi, inda suka hanawa wasu ‘yan majalisa ikon shiga majalisar.

Yace anyi wannan ba don komai ba sai domin yunkurin sauya Shugabancin majalisar dattawa da ake son yi ko ta halin yaya.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja. Ya gargadi Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo akan taka dokokin majalisa da kuma yiwa harkokin demokaradiyya karan tsaye da yi musu katsalandan.

“Ina yiwa Shugaba Buhari da mataimakinsa gargadi akan su dena fakewa da guzuma domin su harbi karsana. DOmin su sun rantse ne zasu kare tsarin mulki kuma zasu yi gaskiya ba tare da nuna wani banbamci tsakanin kowa ba”

 

LEAVE A REPLY