Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakarda tsohon Ministan watsa labarai Jarry Gana da jiga jigan jam’iyyar PDP na kasa sun kaiwa tsohon Gwamnan jihar Filatu Jonah Jang ziyara a gidan kurkuku da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta gurfanar da shi inda kotu ta tura shi gidan maza.

Kotuta bayar da umarnin tsare Jonah Janga a gidan yari ne bayan da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan a a gabanta a ranar 16 ga watan Mayu.

Hukumar na zargin tsohon Gwamna Jang da yin sama da fadi da kudin da suka kai kimanin Naira biliyan 6.3 a zamanin daa yake rike da mukamin kujerar Gwamnan jihar Filatu.

 

LEAVE A REPLY