Daga Hassan Y. A. Malik

Akalla kwaroron roba sama da dubu 200 ne kungiyar lafiya ta ‘Aids Healthcare Foundation’, AHF ta raba a fadin jihar Binuwe don taya al’ummar jihar murnar zagayowar ranar kwaroron roba ta duniya.

AHF ta al’amura na mako guda a bikin na bana da suka hada: gwajin cutar kanjamau da kuma wayar da kan jama’a game da cutar ta kanjamau a kananan hukuma 7 na jihar Binuwe

Kodinatan shirin, Dakta Shu’aiba Joseph, a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a yau Talata, a wajen bikin rufe taron na bana, ya bayyana cewa, AHF ta raba kwaroron roba guda 100,000 a kwaryar birnin Makurdi.

Ragowar 100,000 na kwaroron robar, an raba su ga al’ummar kananan hukumomi 7 da aka gudanar da wayar da kan.

Dakta Shu’aibu ya ci gaba da cewa, sun yi nasarar yi wa matasa gwajin cutar kanjamau kamar yadda suka tsara za su yi tun kafin su faraa zagayen na bana.

Shugaban kwamitin kar ta kwana kan cutar kanjamau na jihar Binuwe, Mista Gideon Dora, ya ja hankalin al’ummar jihar da su dauki yawo da kwaroron roba kamar wani ado da duk inda za su yana tare da su.

Mista Gideon, wacce Regina Ameh ta wakilta, ya ce amfani da kwaroron roba zai taimaka wajen daukar cikin gaba da fatiha tare vkuma da yada cututtukan da ke da alaka da jima’i kamar su kanjamau da dai sauransu.

LEAVE A REPLY