Marigayi Farouk Abubakar

Daga karshe an tsamo gawar Farouk Abubakar dalibin jami’iar kimiyya da fasaha ta Wudil dake jihar Kano, a ruwan Wudil, wanda DAILY NIGERIAN HAUSA a jiya ta baku labarin yaddadalibin ya nitse a ruwa aka kasa samun wadan da zasu dauko shi saboda dare yayi.

Washe garin ranar da dalibin ya nitse a ruwan, ranar Juma’a anci  nasarar dauko gawarsa a ruwan, inda kuma aka yi masa suturu kamaryadda addinin Musulunci ya tanadar aka kuma yi masa jana’iza.

Rasuwar wannan dalibi dai ta harzuka daliban jami’ar, inda suka fito zanga zanaga suna kone kone akan hanyar da ta hada garuruwan Gaya da Wudil, sakamakon kin taimakawa wajen tsamo dalibin a lokacin da ya nitse a ruwan da ‘yan garin na Wudil suka yi, bisa dalilin cewar dare yayi.

Tuni dai Shugaban jami’ar Shehu Alhaji ya bayar da hutun rana kun Alhamis da Juma’a a jami’ar domin yin jimamin rashin wannan dalibi da aka yi a kogin na Wudil.

LEAVE A REPLY