Faith Danjuma, yarinyar da akaiwa ciki

Ma’aikatar ilimi ta jihar Naija ta sallami wani mataimakin shugaban makaranta sakamakon samunsa da laifin yiwa wata ɗalibarsa ciki mai suna Faith Danjuma.

Da yake zantawa da manema labarai a Minna babban birnin jihar Naija, babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta jihar, Yahaya Garba, ya bayyana cewar, tuni aka sanar da babban akawu na jihar Naija domin shaida masa abinda ya faru daga ma’aikatar kula da manyan makarantu ta sakandire, domin biyan mataimakin shugaban makarantar rabin albashinsa.

Kamar yadda yace, bayan da ma’aikatar ilimin ta sami rahoton abinda malamin ya aikata a ranar 28 ga watan Mayu na cewar malamin ya yiwa mata daliba ‘yar aji 3 ciki, ma’aikaytar ilimi ta kafa kwamiti domin bincikar gaskiyar lamarin.

Kwamitin mutum 8 aka kafa karkashin jagorancin Zainab Kolo, mataimakiyar shugaba a makarantar da Malamin ya fito, domin yin bincike na tsakani da Allah kan abinda aka zargi Malaman akai.

Kwamaitin dai ya gano cewar, Faith Danjuma tana dauke da juna biyu mai kimanin sati 7 da kwana 6, inda binciken likitoci ya tabbatar da cewar zata iya haihuwa a watan Nuwambar nan, kuma cikin na shi mataimakin shugaban makarantar ne.

A dan haka ne, kwamitin ya tursasawa mataimakin shugaban makarantar daukar alhakin yin wannan ciki, tare da kula da dukkan dawainiyarsa, har zuwa haihuwar yarinyar. Sannan kuma kwamitin, ya bayar da shawarar a sauyawa malamin wajen aiki zuwa makarantar maza, idan an tabbatar da zargin da aka yiwa Malamin ya zama gaskiya.

Har ya zuwa yanzu dai abin na matakin zargi ne, bai tabbata ba. Idan bincike ya tabbatar da cewar Mataimakin Shugaban makarantar shi ne ya yiwa dalibar ciki, ma’aikatar Ilimi zata san hukuncin da ya dace da shi.

LEAVE A REPLY