Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

Mzauna garin Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan yunkurin Gwamnati na dawo da dokar ta baci a Maiduguri zuwa 8:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

Gwamnatin nihar Borno a ranar litinin ta bayyana yunkurin sake duba dokar ta-baci da aka sanya a jihar daga 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe, a sabida yadda lamuran tsaro ke neman jagulewa a jihar.

Muhammad Bulama, Kwamishinan harkokin da suke shafi walwalar jama’a da yada labarai ya bayyana cewar kara lokacin dokar ta-bacin na dan lokaci kadan ne, domin baiwa dukiyoyi da rayuka kariya.

Bulama ya kara bayyana cewar, wannan yunkuri ya samu ne sakamkon shawarwari da aka baiwa Gwamnati daga jami’an tsaron Lafiya Dole.

Wani sashe na mazauna birnin Maiduguri sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, cewar an mayar musu da al’amura baya matukar aka cigaba a haka.

Wani mazaunin birnin, Muhammad Idris, ya bayyana cewar dawo da dokar ta-bacin ba shi ne abinda ya dace ba domin samar da dawwamammen zaman lafiya.

“A shekara biyu da ta wuce, mun ji dadin kyautatuwar al’amuran tsaro, musamman yadda muke iya yin mu’amalolinmu da daddare”

“Batun sake dawo da wannan dokar, ba komai zai yi sai sake mayarda hannun agogo baya, kuma mutane zasu fuskanci tsananin rayuwa sosai”

Wani mai sana’ar sayar da gasasshen NamaIbrahim AMinu,  yace dawo da wannan dokar zai nakasta harkokin sana’arsa.

“Dawo da wannan doka ba komai zai yi sai mayar mana da dan kasuwancinmu baya, bayan mun sha wahalar farfado da shi da kyar” A cewarsa.

Amma a nata bangaren, Hauwa Musa, ta bayyana cewar, dawo da lokacin dokar ta bacin, tunani ne mai kyau, kuma zai sake kyautata al’amuran tsaro a jihar.

Hauwa ta kara da cewar, hare haren baya bayan nan da ake kaiwa, sun jawo rashin nutsuwa da rashin aminci a tsakanin al’ummar wannan jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito hare haren da ‘yan kungiyar Boko Haram suka dinga kaiwa a ‘yan kwanakinnan, a yankin gefen Maiduguri

LEAVE A REPLY