Daga Hassan Y.A. Malik

Kwamishinan ilimin jihar Yobe, Mohammad Lamin, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta rufe makarantar ‘yan mata ta kimiyya da fasaha ta G.G.S.T.C Dapchi sai baba ta gani

Kwamishinan ya fitar da wannan sanarwa ne jiya Litinin a babban birnin jihar, Damaturu.

Kwamishin a cikin sanarwar ya bayyana cewa, “Har yanzu akwai sama da ‘yan mata 100 da ba mu ji duriyarsu ba. Su kuma wadanda aka samu ma, suna cikin halin dimuwa.”

Lamin ya ci gaba da cewa makarantar za ta ji gaba da kasancewa a rufe har sai yanayin daliban ya daidaita kuma abubuwa sun dan huce a zukatan al’umma da iyaye da daliban makarantar.

Gwamnatin tarayya, a ranar Lahadin da ta wuce ta bayyana cewa, dalibai 110 ne cikin dalibai 906 da makarantar ke da su suka yi batar dabo bayan harin na ranar Litinin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a watan Disambar 2015 ya bayyana cewa gwamnati ta murkushe mayakan Boko Haram, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ga daukacin kasar Nijeriya.

LEAVE A REPLY