Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa game da yawan kashe-kashen jama’a a Najeriya, inda ta ce an kashe fiye da mutane 1,800 a bana kawai.

Ta ce ba ta jin dadin yadda ake samun asarar rayuka sanadiyyar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, da na kabilanci, da hare-haren ‘yan fashi, da kuma rikicin Boko Haram.

Sai dai kungiyar ta dora alhakin yawaitar hare-haren da kuma mayar da ramuwar gayyar kan gazawar hukumomin tsaron kasar.

Wata sanarwar, wadda mai magana da yawun kungiyar a Najeriya, Isa Sanusi, ya sa wa hannu, ta ce akalla mutum 1,800 ne aka halaka daga watan Janairun da ya gabata zuwa Yuni a jihohi 17 na kasar.

Kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu, “ya nunka na gaba dayan shekarar da ta gabata, wanda aka kiyasta cewa ya haura 800,” a cewarsa.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duk da kalubalen tsaron da ake fuskanta gwamnatinsa ta “cimma muhimman nasarori” a fannin.

Har ila yau kungiyar ta ce a al’amari na baya-bayan nan da ya auku a jihar Filato, ‘yan bindiga sun kai wa kauyuka 11 hari a ranar Asabar da ta gabata, suka kwashe tsawon sa’o’i bakwai suna ta’adi, inda suka kashe mutane akalla 200 a kauyukan.

“Kuma jama’ar wuraren ba su samu wani dauki daga jami’an tsaro ba.” Al’amarin da kungiyar ta bukaci a gudanar da bincike a kansa.

Duk da cewa an tura rundunonin tsaro, ciki har da sojoji, a jihohi fiye da 30, karuwar wadannan hare-hare suna nuni ne da cewa, duk wani mataki da hukumomin Najeriya ke dauka ba ya yin tasiri, a cewar kungiyar.

Daga nan, kungiyar ta jaddada bukatar gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaggauta daukar matakin hukunta mutanen da ke da alhakin wannan ta’adi da aka yi a jihar Filato.

BBCHAUSA.COM

LEAVE A REPLY