Gwarzon Musabaka na bana, Amiru Yunusa

Amiru Yunusa dan shekara 20 daga jihar Bauchi shi ne ya zama Gwarzon Musabakar karatun Al-Kurani mai tsarki a bana da aka kammala a jihar Katsina, a gasar karatun Kur’ani karo na 32.

Hakakuma, Amina Ahmad daga jihar Borno ita ce Gwarzuwar musabakar Alkurani ta bana a bangaren mata.

Babban kodineta na musabakar gasar karatun Al-Kur’ani ta kasa Sani Yunus Birnin-Tudu shi ne ya bayyana sakamakon gasar da aka yi.

Gasar dai ta kunshi tilawar Al-Kur’ani da kuma tafsirinsa da harshen larabci.

Ya bayyana cewar akalla mutane 360 ne daga jihohi 32 suka shiga gasar karatun Al-Kur’ani ta bana.

Malam Sani Birnin-Tudu ya bayyana cewar yaran guda biyu sune suka samu nasara daga bangaren mata da kuma bangaren maza a gasar da aka shafe makwanni ana karawa tsakanin ‘yan musabakar.

Wadan da suka yi nasarar gasar sun samu Kyautar sabuwar mota da kwamfutar tafi da gidanka da kuma zunzurutun kudi Naira 500,000 kowannensu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar a sassa biyar da aka yi gasar a cikinsu, kowanne sashi wanda yayi nasarar zamowa zakara ya samu kyautar sabuwar mota.

 

LEAVE A REPLY