Rotimi Amaechi

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ribas, kuma tsohon Gwamnan jihar Ribas, Ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi an bayyana cewar shi ne mutumin da yafi kowa talauci a cikin ministocin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, a cewar wani hadimin minista Kinsley Wali.

Wali ya bayyana hakan ne a ranar bikin tunawa da ranar da aka yi zaben 12 ga watan Yuni, wanda ake ikirarin Abiola yaci aka murde, taron da wasu magoya bayan jam’iyyar APC  suka shirya a jihar Ribas.

A cewar hadimin, bisa irin yanayin Amaechi na rashin son almubazzaranci ya sanya shi zama minista mafi fama da talauci a kunshin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Mutum mai matukar kankan da kai da rashin son tara abin duniya. A cewar Kinsley Wali.

 

LEAVE A REPLY