Tsohon Gwamnana jihar Binuwai George Akume

Tsohon Gwamnan jihar Binuwai, kuma Sanata a majalisar dattawan najeriya, George Akume ya bayyana rashin jin dadin al’ummarsa ga Shugaba Buhari akan halin ko in kula da ya nuna a kisan gilla da aka yiwa Tubawa a jihar.

Mista Akume, ya tunawa Shugaba Buhari cewar, mutanan jihar Binuwai gaba daya kwata suka nuna soyayya da goyon baynsu ga Shugaba Buhari ta hanyar zabarsa a zaben da ya gabata na 2015, duk kuwa da cewar Shugaban majalisar dattawa na lokacin David Mark yana tare da jam’iyyar PDP kuma dan asalin jihar ne.

Ya nemi Shugaba Buhari da ya gaggauta kawon karshen kisan da ake yiwa Tubawa a jiharsu ta Binuwai.

Yace “Ranka ya dade, zaka iya tunowa, Sanata David Marka yana Shugaban majalisar dattawa,kuma Suswam yana Gwamnan jihar Binuwai, al’ummar Tibi suka yi watsi da su suka zabe ka a 2015”

“Har zuwa yanzu babu wani aikin Gwamnatin tarayya ko guda daya a jihar Binuwai, Gwamna Ortom bai yi wata doka ba, al’ummar jihar Binuwai sune suka nemi a yi doka, JS Tarka yayi yaki domin hadin kan wannan kasar, Shugaban kasa, al’ummar Tibuawa sam basa farinki ko maraba da kai akan yadda ka nuna musu halin ko in kula a lokacin da Fulani ke yi musu kisan gilla”

LEAVE A REPLY