Kungiyar nan mai fafutikar kare ‘yancin mata da yara ta WRAPA, ta baiwa alkalan kotunan Shari’ar Musulunci daga yankin Arewa maso yamma horo na musamman akan dokokin iyali a Musulunci.

Horon wanda aka yi kwana biyu ana yinsa wanda mahalartan suka fito daga Zamfara da Jigawa da Sakkwato da Kebbi da Kano da kuma Katsina.

Shugabar tsara shirin Hajiya Saudatu Mahadi ta shaidawa manema labarai akan yadda akungiyarsu ta gudanar da wannan shiri a Gusau a ranar laraba. Inda tace makasudin wannan horo domin a ilmantarda alkalan kotunan Shari’ah kan muhimman ayyuan da suke a gabansu.

Tace wannan horo zai bayyana manufofin Shariah ne kan ‘yancin mata a addinin Musulunci.

Hajiya Saudatu Mahadi tace alkalan da suka fito daga jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara an sanya Gusau ya zama inda zasu karbi wannan horo.

“A yanzu haka da nake magana da ku, akwai wani sashi na mahalarta wannan taro da yake gudana yanzu haka a birnin Dutse ta jihar Jigawa,inda Alkalai 44 suke samun horo daga jihohin Kano,Katsina, da kuma Jigawa”

“Babban makasudin wannan horo shi ne, domin mu ilmantar da su akan sabon shirinmu na dokokin tsarin iyali a Musulunci”

 

LEAVE A REPLY