Mai Shariah Gideon Kurada shi ne Jojin babbar kotun tarayya dake Kaduna, kuma ya sanya ranar Alhamis din nan domin sauraren cigaba da Shariar da ake yiwa jagoran ‘yan Shiah El-Zakzaky tare da matarsa Zinatu akan tuhumce tuhumcen da ake yi musu.

Tun da fari dai Gwamnatin jihar Kaduna ce kaarkashin jagorancin Gwamna Nasiru El-Rufai ta gabatar da kara gaban babbar kotun inda take tuhumar Jagoran ‘yan Shiah akan wasu tuhumce tuhumce guda takwas da take yi  masa tare da mai dakinsa.

Sai dai a yau da ‘yan jarida suka je harabar kotun domin shaida zaman kotun na yau, ‘yan sanda sun hana dukkan ‘yan jarida shiga harabar kotun domin sauraren karar.

Sai dai kumma, lauyan da yake kare Zakzaky a wannan shariar Femi Falana SAN, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, cewar alkalin da yake lura da wannan Shariar yayi batan dabo.

Haka kuma, Falana ya bayyana cewar tun da abin ya zama haka, da shi da sauran lauyoyin da suke kare bangaren wadan da suka shigar da kara, sun sake ajiye ranar 11 ga watan Yuli a matsayin ranar da zasu sake dawowa kotu.

Falana yayi Allah wadai da ‘yan sanda da suka hana ‘yan jarida shiga harabar kotun domin dauko rahoton abinda ke faruwa.

Yace babu wata doka da ta baiwa ‘yan sanda damar hana wani shiga  harabar kotun domin duk dan kasa yana da ‘yancin ya shiga ya shaida zaman kotu.

NAN

LEAVE A REPLY