Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osibanjo

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo a ranar laraba ya bayyana cewar Najeriya na bukatar dalar Amurka biliyan 2 (Naira biliyan 610) domin dawo da titin jirgin kasa da ya tashi daga Legas zuwa Kano, domin inganta harkar cinikayya tsakanin kudu da Arewa.

Mista Osibanjo ya bayyana hakan ne a taron habaka cinikayya tsakanin jihar Legas da kuma Kano, wanda aka gudanar a Legas. A cewarsa, Gwamnatin tarayya tare da hadin guiwar wani kamfani mai zaman kansa, zasu duba yuwuwar kulla alaka domin samar da layin dogon dan habaka kasuwancin yankin kudu da Arewa.

Mataimakin Shugaban kasar, ya nuna jin dadinsa kan wannan alakar kasuwanci da aka kulla tsakanin jihar kano da jihar Legas, a cewarsa, wannan zai baiwa ‘yan kasuwa daga ko ina a duniya damar zuba jari a jihohin biyu, wanda al’ummar zasu jihohin biyu ci moriya.

“Ina da kwarin guiwar cewar, hadin kai tsakanin jihohin Kano da Legas, zai habaka tattalin arzikin ita kanta Gwamnatin tarayyar najeriya, tare da sanya mafitar halin ha’ula’in da tattalin arzikinmu yake ciki”

A nasa jawabin, fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewar “Daga zarar matatarmu da muke ginawa ta gama kammaluwa zamu samar da takin zamani da mai da dangoginsa, zamu iya samarwa da Gwamnati kimanin Naira tirliyan 8 a cikin shekara daya”

A lokacin da yake nasa jawabin, mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na biyu ya bayyana cewar “Idan jihar Kano da Legas suka hada kai wajen fuskar kasuwanci, ba wai kawai magana za’a yi ta batun tattalin arzikin Najeriya ba, har ma da yankin kasashen Afurka ta yamma baki daya”

Manya manyan mutane ciki har da Sarakuna daga yankin kasashen Yarabawa ne suka halarci wannan taron.

LEAVE A REPLY