Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC domin yin takarar Gwamnan jihar Sakkwato.

Ahmed Aliyu daya ne daga cikin na hannun daman Tsohon Gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wammako, kuma bai bi Gwamna Tambuwal zuwa PDP ba.

Ahmed Aliyu yayi Nasara da kuri’u 2282 inda ya kada abokin takarar sa Farouk Malami Yabo da rays mai yawa. Wasu na ganin cewar tsohon Gwamnan jihar Aliyu Wammako be ya tursasawa masu zaben su zabi Ahmed Aliyu.

LEAVE A REPLY