Ma’aikatan kashe gobara na hukumar kashe gobara ta jihar Adamawa sun ci nasarar kashe gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Yola a jiya laraba.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Adamawa, Adamu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a birn Yola.

Adamu yace, jami’an sun samu nasarar isa kasuwar lokacin da suka samu kiran gaggawa na cewar gobara ta tashi a kasuwar, kuma sun ci nasarar kashe wutar.

“Wuatar dai bata yi wata mummunar illa ba, illa kawai wasu mashinan aikin gona da ta kone da wasu shaguna kalilan”

Ya kara da cewar, babu hasarar rai ko daya a sanadiyar wannan gobara, sanna babu wani da ake zaton ya samu mummunan rauni sanadiyar tashin wutar.

Har ya zuwa yanzu dai ba’a kai ga samun kididdigar adadin dukiyar da gobarar ta halaka ba, domin masu shaguna na cigaba da zuwa suna duba irin barnar da ta yi musu.

NAN

LEAVE A REPLY