Marigayi Alhaji Lawal Kaita

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai nuna juyayinsa da alhininsa na rashin tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita, wanda ya rasu yana da shekaru 85.

Gwamna el-Rufai, a wani sakon ta’aziya da ya aikewa da iyalan tsohon Gwamnan, wanda mai magana da yawunsa SamuelAruwan ya bayyana, Gwamnan ya bayyana tsohon Gwamnan a matsayin mutum mai kwarjini da tallafawa kokarin shugabanni.

“Alhaji Lawal Kaita, mutume na kwarai kuma gwani,ya taimaki al’umma lokacin da ya zama Gwamnan tsohuwar jihar kaduna, ya karar da rayuwarsa gaba daya domin yin hidimar al’umma”

“A matsayinsa na zababben Gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, ya taimaka matuka wajen ciyar da jihar Kaduna gaba, musamman ta fuskar hadinka da kuma zaman lafiya da cigaban jihar Kaduna”

“Alhaji Lawal Kaita, mutum ne nagari abin koyi ga kowa, musamman ga shugabannin gobe masu tasowa”

Haka kuma, Kungiyar magabatan Arewa ta ACF, ta bayyana cewar ta samu labarin rasuwar Alhaji Lawal Kaita cikin dimuwa da kaduwa, a matsayin na daya daga cikin wadan da suka kafa kungiyar ACF dole muji kaduwa da labarin rasuwarsa.

“Najeriya gaba daya tayi rashin gwarzo abin koyi,kwarrren dan siyasa, kuma shi baya ne goya marayu”

“Marigayi Lawal Kaita, za a jima ana tunawa da shi musamman wajen halayensa na kirki da nuna son al’umma da cigabanta, da kuma yadda ya damu da batun cigaban Najeriya ta fuskar zaman lafiya”

“Muna adduar Allah ya jikansa ya gafarta masa, yasa Aljannah ce makomarsa” A sakon da kungiyar ACF ta fitar ta bakin Sakataren watsa labaranta Muhammad Ibrahim.

NAN

LEAVE A REPLY