Sanata Shehu Sani

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a jiya Talata ya yi dan biki ga jam’iyyarsa ta APC da abokiyar hamayyarta ta PDP bisa jerin sunaye da jam’iyyun biyu suka fitar na barayin gwamnatin Nijeriya.

Shehu Sani ta shafinsa na twitter ya yi kira ga APC da PDP da su fitar da jerin sunayen mahasumai (wadanda basu taba aikata wani sabo ba) a jam’iyun biyu.

“Jam’iyyun biyu sun nishadantar da kasar da jerin sunayen barayin gwamnati.”

“Yanzu abinda ya rage shi ne su wallafa mana sunayen ‘Mahasumai’ wadanda basu taba aikata wani laifi ba,” inji Shehu Sani

Sanatan ya yi bayani kan batun yadda rashin tsaro ke kara ta’azzara a jiharsa ta Kaduna, inda ya bayyana lamarin da cewa ya kai kololuwar da bai taba kaiwa ba tunda aka kirkiri jihar.

“Wadanda ke amfana daga wannan yanayi na rashin tsaro da suka jefa Kaduna a ciki, su sani cewa akwai ranar kin dillanci duk kuwa da cewa suna lullube da kariyar alfarmar mulki a yau.”

LEAVE A REPLY