Shugaban jibiyar Alfurqan kuma babban limamin Juma'aa na Masallacin Alfurqan Kano, Dr. Bashir Aliyu Umar

Babban limamin juma’a na Masallacin Alfurqan, kuma Shugaban cibiyar Alfurqan Charitable Foundation, Dr. Bashir Aliyu Umar, ya bayyana cewar abin kunya ne a ce an soke tsarin Amirul Hajji a lokacin aikin Hajji a Najeriya.

Malamin yayi wannan bayani ne a ranar Lahadi lokacin da yake gabatar da Tafseirin Alkurani mai girma a Masallacin Alfurqan Kano. A cewarsa “Amirul Hajji tuun zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam al’ummar Musulmi take da Amirul Hajji”

“A yayin aikin Hajji na farko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ya wakilta Sayyaduna Abubakar ya kasance Amirul Hajji ga dukkan Musulmi, kuma ya jibanci al’amuran aikin Hajji ga al’ummar Musulmi”

“A yayin da yayi aikin Hajjinsa na farko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shi ne da kansa ya kasance Amirul Hajji, dogara da wannan ya zama koyi da Sunnarsa SAW, sanyawa al’ummar Musulmi Amirul Hajji”

“Amma abinda wannan Gwamnatin ta yi na soke tsarin tura Amirul Hajji abin kunnya ne, domin shi AMirul Hajji shi ne wakilin dukkan Musulmin Najeriya, wanda duk suke da hannu wajen cire tsarin Amirul Hajji a Najeriya sun ji kunya kuma ba su kyautawa al’ummar Musulmin Najeriya ba” A cewar Dr. Bashir Aliyu Umar.

 

LEAVE A REPLY